Isa ga babban shafi
Afrika

Ana zargin 'Yan awaren Kamaru da azabtar da mutane a yankunan su

A kasar Kamaru, wani hoton bidiyo da yanzu haka ke yawo a kaffafen sada zumunta na Intanet, na nuna yada mayakan ‘Yan aware ke gallazawa wasu mata uku.

Masu zanga-zanga a yankin Ambazonia
Masu zanga-zanga a yankin Ambazonia Reuters TV/Reuters
Talla

Hoton bidiyon mai sosa rai, wanda jaridun kasar ta Kamaru suka maida hankali a kai, ya nuna yadda mayakan‘yan aware na yankin kasar da ake amfani da Turancin Ingilishi da ke neman ballewa domin kafa jamhuriyar Ambazonia, da ake kira Amba Boys, na amfani da sanduna da bulala wajen dukan wasu mata uku.

Biyu daga cikin matan na dauke da jijirai da basu zarce watanni 6 ba, a tsakiyar ranar, a wani lokaci ma saida daya matar ta saki dan nata don tsananin duka.

Rahotanni sun bayyana matan uku a matsayin ma’aikatan wani asibiti a yankin, wanda maharan suka zarga da sayarwa dakarun gwamnati da ke yaki da su abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.