Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan aware sun yi garkuwa da Fasinja 30 a Kamaru

Akalla Fasinjoji 30 hukumomin kasar Kamaru suka tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su cikin daren juma’ar da ta gabata a kan babbar hanyar Fundong zuwa Bamenda da ke yankin arewa maso yammacin kasar mai fama rikicin ‘yan aware masu kokarin ballewa.

Jami'an tsaron Kamaru a yankin 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi
Jami'an tsaron Kamaru a yankin 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi REUTERS/Joe Penney
Talla

Hukumomin kasar da suka tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata sun bayyana cewa lamarin ya faru ne cikin daren juma’a lokacin da motoci 3 dauke da fasinjoji suka tashi daga Fundong zuwa Bamenda.

Guda cikin direbobin motar Safar 3 da aka yi garkuwan da Fasinjan su, Samuel Nkwain ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar wadanda mambobin ‘yan aware ne sun tsayar da motocinne a dai dai Belo inda suka da umarci kowa ya fito daga Motar tare da daga katin shaidarsa sama.

A cewar Direban motar, ‘yan bindigar sun tisa keyar mutanen su fiye da 30 zuwa tsakar Daji, kuma kawo yanzu ba a san inda su ke ba.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, Garkuwa da fasinjan na zuwa ne bayan wata arangama tsakanin bangarori biyu na ‘yan awaren wadda ta kai ga kwace makaman bangare guda.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci kamfanin dillancin Labaran kasar ya sakaya sunansa, ya ce bangaren da suka yi garkuwa da fasinjan sun ce za su iya sakin mutanen 30 matukar daya bangaren ya mika musu makamansu.

Mahukunta a kasar ta Kamaru dai sun bayyana cewa an dakatar da zirga-zirga a yankin da abin ya faru yayinda aka baza jami’ai don laluben mutanen.

Batutuwa masu alaka da garkuwa da mutane kisan dauki dai-dai da kuma rikice-rikice na ci gaba da ta’azzara a yankin mai amfani da turancin Ingilishi wanda ke karkashin kasar ta Kamaru mai amfani da Faransanci.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana cewa yanzu haka akwai mutane dubu 430 da suka tsere daga muhallansu sanadiyyar rikicin yankin, tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin yaki da su a cikin watan Nuwamban shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.