Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane da dama ne suka mutu a harin Al Shebab a Kismayo

Majiyar tsaron kasar Somalia ta sanar da kawo karshen samamen da wasu yan kungiyar Al Shebab suka kai wani Otel tareda yi garkuwa da mutane a wannan wuri dake Kismayo.

Jami'an tsaro dake suturi a Somalia
Jami'an tsaro dake suturi a Somalia RFI/Sébastien Németh
Talla

Yan Al Shebab dauke da manyan makamai sun yi garkuwa da wasu mutane a wani gidan Otel dake Kismayo.

Jami’an tsaro sun share daren jiya suna kokarin kubutar da mutanen dake cikin wanan Otel.

Majiyar tsaro Somalia ta bayyana mutuwar mutane 12 daga cikin mutanen da suka rasa ran su akwai wani Minista da wani dan Majalisa, yayinda wasu 30 suka samu raunuka.

Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin tanttance masu bayar da goyan baya zuwa yan kungiyar Al Shebab a wadanan hare-hare dake hadasa mutuwar jama’a da dama a kasar ta Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.