Kamaru: Gwamnati ta saki yan adawa 39 daga gidan yari
A Kamaru gwamnatin kasar ta saki wasu 'yan adawa 39 daga gidan Yari a daren ranar Juma’a, kamar yadda jam’iyyar adawa ta MRC ta tabbatar.
Wallafawa ranar:
Sai dai fursunonin 'yan adawar da aka saki, ba sa cikin 104 da ake shirin gurfanar da su gaba kotun sojin kasar, cikinsu harda lauya kuma daya daga cikin jagororin jam’iyyar adawar ta MRC Maurice Kamto, wadanda ake zargi da karya dokokin kasa.
A karshen watan Janairu da ya gabata, aka kame Maurice Kamto tare da wasu magoya bayansa 150, saboda zanga-zangar adawa da gwamnati da suka jagoranta a wasu manyan biranen Kamaru.
Jagoran yan adawar ne ya zo a matsayi na biyu, yayin zaben shugabancin kasar da ya gudana a watan Oktoban 2018, wanda shugaba mai ci Paul Biya ya lashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu