Wannan sanarwar na zuwa ne mako guda bayan cimma yarjejeniya tsakanin sojin da shugabannin masu zanga zanga na kafa gwamnatin rikon kwarya.
Janar Jamal Omar dake majalisar mulkin sojin yace an kama manyan sojoji daga rundunar sojin da hukumar leken asiri da kuma yan sandan farin kaya da suka yi yunkurin, cikin su harda wadanda suka yi ritaya.
Janar Omar ya bayyana cewar wannan wani yunkuri ne na dakile shirin kafa gwamnatin rikon kwaryar da aka amince da ita a kasar ta Sudan.