Isa ga babban shafi

AU ta nuna damuwa da katsalandan din kasashen Turai a Libya

Kungiyar kasashen Afirka ta AU ta bayyana damuwar ta kan yadda ake samun katsalandan daga kasashen waje a Libya, inda ta bukaci kafa wani kwamitin na musamman tsakanin Jakadun Majalisar Dinkin Duniya da na ta domin yin aikin samo hanyar magance rikicin kasar.

Firaministan Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Fayez al-Sarraj
Firaministan Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Fayez al-Sarraj AFP
Talla

Kungiyar ta ce kwamitin zai yi aiki wajen aiwatar da shirin zaman lafiyar Libya kamar yadda masu shiga tsakanin suka shata tare da shugabannin kungiyoyin dake rikici a kasar.

Rahotanni sun ce an samu zazzafar mahawara wajen taron kungiyar, ko da dai shugabanta AbdelFatah al Sisi kuma na hannun daman Khalifa Haftar ya kauracewa zaman taron.

Libya dai ta koma cikin yakin basasa ne tun bayan da Khalifa Haftar mai rike da galibin yankunan kasar ya kaddamar da farmakin kwace birnin Tripoli cikin watan Aprilu.

Majalisar Dikin Duniya dai ta bayyana cewa fiye da mutane dubu guda sun rasa rayukansu a sabon rikicin na Libya yayinda wasu fiye da dubu 75 suka tsere daga kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.