Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatin Mali za ta tura sojoji dubu 3, 500 zuwa tsakiyar kasar

Fira ministan Mali Boubou Cisse ya sha alwashi karfafa matakan tsaro a Yankin tsakiyar kasar mai fama da tashin hankali.

Sojojin Mali a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Mali.
Sojojin Mali a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Mali. AFP/ Michelle Cattani
Talla

Bayan kamala ziyarar gani da ido na kwanaki 5 a Yankin, wanda Jami’in jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa kan karuwar hare hare, Cisse yace za’a kara dakaru 3,500 a Yankin, inda ya kara da cewa tuni 1,500 suka isa wurin.

Majalisar Dinkin Duniya tace tsakanin watan Mayun bara zuwa watan na bana akalla mutane 70,000 suka tsere daga Mopti da Segou domin tsira da rayukan su.

Rahotanni sun ce akasarin kauyukan dake Yankin sun zama kufai, saboda babu kowa a cikin su.

A karshen watan Yuni kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara nazari game da bukatar da Faransa ta gabatar, domin sanya takunkumai a kan wasu mutane biyar da ke haddasa tarnaki wajen samar da zaman lafiya a Mali, cikinsu har da wani dan majalisar dokoki daga jam’iyya mai mulkin kasar.

Daga cikin mutanen biyar akwai Houka Houka Ag Alhousseini wanda jagoran masu da’awar jihadi ne a Tumbuktu, sai kuma Mahri Sidi Amar Ben Daha wanda ya assasa ayyukan jihadi a garin Gao duk a Arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.