Afirka: Najeriya ba za ta gaggauta shiga kasuwancin bai-daya ba
Shugaban Najeriya Muhd Buhari ya ce kasar ba za ta gaggauta shiga cikin yarjejeniyar huldar kasuwancin bai-daya tsakanin kasashen Afirka ba, har sai ta kammala nazari kan shawarwarin masana, dangane da amfani da kuma akasinsa da Najeriya za ta fuskanta cikin Yarjejeniyar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yarjejeniyar kasuwancin za ta bada damar samar da babbar kasuwa guda ta kasashen Afrika, shige da ficen kayayyaki da yan kasuwa ba tare da shamaki ba, sai kuma samar da takardar kudin bai-daya da kasashen nahiyar za su rika amfani da shi.
A watan Maris na shekarar 2018 kasashen Afirka suka rattaba hannu kan somaaiwatarda zangon farko na yarjejeniyar a birnin Kigali.
Zalika yarjejeniyar, ta bada damar dage haraji daga kan kashi 90 na kayayyakin da kasashen Afirka ke kaiwa kasuwannin junansu, daga bisani kuma ya a dage dukkanin wani haraji daga kan kayayyakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu