Sama da mutane miliyan 10 na fama da cutar hanta a Afirka

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewar sama da mutane miyayan 10 sukayi fama da cutar hanta ko Hepatitis a shekarar 2015 a nahiyar Afrika, kuma sama da miliyan 4.8 yara kanana ne.
Hakazalika tace a kowani shekara mutane 200 ne ke mutuwa daga cutar,wanda kuma babban abun takaici kamar yadda zakuji cikin wannnan rahoto da Wakilin mu na Abuja Mohammad Sani Abubakar ya hada, a cikin kasashe 47 na nahiyar ta Afrika kasashe 3 ne kawai suka sa himma wajen ganin sun kawar da cutar.