Isa ga babban shafi
Tunisia

Harin kunar bakin wake ya jikkata mutane 9 a Tunisia

Ma’aikatar cikin gida a Tunisia ta tabbatar da tagwayen hare-haren kunar bakin waken da wasu ‘yan bindiga suka kai wanda ya hallaka Dan sanda guda tare da jikkata wasu Karin fararen hula 9, harin da ke zuwa bayan fara fuskantar zaman lafiya a kasar wadda a baya ta yi fama da hare-hare.

Yankin da aka kaddamar da hare-haren mai tazarar mita 200 da Ofishin jakadancin Faransa
Yankin da aka kaddamar da hare-haren mai tazarar mita 200 da Ofishin jakadancin Faransa REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Hare-haren kunar bakin waken wadanda kawo yanzu ba a san wadanda ke da alhakin kaddamar da su ba, na zuwa ne dai dai lokacin da fadar gwamnatin kasar ke sanar da tsanantar rashin lafiya shugaba Essibsi.

Haka zalika harin wanda aka kaddamar gab da misalign karfe 11 na safiyar yau Alhamis ya zo ne dai dai lokacin da ake shirye-shiryen zabe, wanda Tunisian ke fatan samun maziyarta da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa harin farko ya faru ne gab da wani shingen bincike da ke tsakiyar birnin Tunis inda nan ta key a hallaka jami’in dan sanda guda tare da jikka Karin wani baya ga fararen hula da suka samu raunuka.

A cewar ma’aikatar cikin gida ta gwamnatin Tunisian harin na biyu ya faru ne a babban Ofishin ‘yan sanda da ke birnin na Tunis inda dan kunar bakin waken ya tashi bom din da ke jikinsa, tare da jikkata mutane akalla 7.

Yanzu haka dai wasu bayanai sun bayyana cewa, an girke tarin jami’an tsaro a wuraren da aka kaddamar da hare-haren wanda ke da tazarar mita 200 da Ofishin jakadancin Faransa.

Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gida a Tunisian Sofian Zaak ya bukaci al’ummar kasar su kwantar da hankulansu.

Rabon Tunisa da makamancin harin dai tun cikin watan Octoban bara lokacin da wata mata ta tashi bom din da ke jikinta ta hallaka mutane 15 tare da jikkata wasu 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.