Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar-Boko Haram

Boko Haram ta hallaka mutane 20 a iyakar Najeriya da Nijar

Rahotanni daga Najeriya sun bayyana cewa mayakan Boko Haram sun farmaki wani kauye na Ngamngam da ke kan iyakar kasar da Nijar daga jihar Borno tare da hallaka wasu mutane 20 da ke tsaka da aikin gona.

Wasu sojin Najeriya lokacin da suke sintiri gab da kauyen Hausari a jihar Borno
Wasu sojin Najeriya lokacin da suke sintiri gab da kauyen Hausari a jihar Borno REUTERS/Joe Brock
Talla

Harin wanda aka bayyana da mafi muni cikin hare-haren ta'addanci na baya-bayan nan da Boko Haram ke kai wa, na zuwa ne kasa da wata guda bayan shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a wa'adi na biyu, inda kuma ya sha alwashin kammala murkushe matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Rahotannin sun ce yanzu haka al'ummar kauyen na Ngamngam da ke kan iyakan jihar Borno da kasar Nijar, sun tsere zuwa kauyen Damasak da ke kusa.

Wani jami'in agaji da ke cikin jami'an tsaron sa kai masu taimakawa Sojin Najeriyar wajen yakar Boko Haram, Bakura Kachalla shaidawa kamfanin dillancin labarai cewa da hannunsa ya taimaka wajen tattara gawar wadanda harin ya rutsa da su akalla 20.

Kawo yanzu dai kungiyar ta Boko Haram ba ta ce komai game da harin ba.

Ko a makon da ya gabata kungiyar ta Boko Haram ta kai wani kazamin harin kunar bakin wake garin Konduga gab da Maiduguri fadar gwamnatin Borno inda ta hallaka akalla mutane 30.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.