Isa ga babban shafi
Mauritania

'Yan takara shida na fafatawa a zaben Mauritania

A gobe Asabar ne al’ummar Mauritania za su kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa, inda a wannan karon ‘yan takara shida ke fafutukar maye gurbin shugaba Ould Abdel Aziz mai barin gado.

Mutane miliyan hudu ne za su kada kuri'a a zaben shugaban kasar Mauritania
Mutane miliyan hudu ne za su kada kuri'a a zaben shugaban kasar Mauritania RFI/Paulina Zidi
Talla

Dan takarar jam’iyya mai mulki kuma tsohon Ministan Tsaron Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani, na fuskantar kalubale musamman daga bangaren dan takarar babbar jam’iyyar adawa kuma tsohon Firaministan kasar, wato Sidi Mohd. Ould Boubaker.

Wasu alkaluma sun bayyana Ghazouani, tsohon aminin shugaba Ould Abdel Azizi a matsayin wanda ka iya lashe zaben lura da goyon bayan da yake samu daga sama da kananan jam’iyyun siyasa fiye da 20 da kuma ‘yan kasuwa da ke agaza masa, amma duk da haka babban mai adawa da shi, wato Boubaker na yi masa barazana.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Mai fafutukar Kare Hakkin Bil’adama, Biram Ould Abeid da Mohamed, Ould Mouloud da shi ma ya yi fice a adawa da gwamnatin kasar.

Suran ‘yan takarar sun hada da malamin makaranta Kane Hamidou Baba da kuma masanin tattalin arziki, Mohame  Al-Amin al-Wafi.

A cikin watan Janairun da ya gabata ne, shugaba Abdel Aziz ya ce, ba zai sake tsayawa takara ba bayan ya yi watsi da bukatar magoya bayansa ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima da zummar ba shida damar zarcewa a wa’adi na uku.

Mutane miliyan uku daga cikin daukacin al’umar kasar miliyan hudu ne suka cancaci kada kuri’a a zaben na gobe Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.