Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari ya nada sabon shugaban kamfanin mai na NNPC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mele Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin man fetur din NNPC domin maye gurbin Maikanti Baru da wa’adin sa ke karewa ranar 7 ga watan gobe.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sanarwar da kamfanin man NNPC ya fitar da kan sa ya bayyana cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mele Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin man kasar, yayin da ya kuma bayyana nadin wasu manyan manajoji guda 7 da zasu taimakawa Kyari gudanar da ayyukan sa.

Manajojin guda 7 sun hada da Ronald Onorriode Ewubare da Mustapha Yunusa Yakubu da Yusuf Usman da Lawrence Nwadiabuwa Ndupu ad Umar Isa Aliyu da Adeyemi Adetunji da Faruk Garba.

Kafin wannan nadi, Kyari ne Janar Manajan dake kula da kasuwancin danyan man Najeriya kana kuma wakilin kasar a kungiyar kasashe masu arzikin mai.

Sanarwar mai dauke da hannun Ndu Ughamadu tace Maikantai Baru zai kammawa wa’adin sa ne ranar 7 ga watan gobe, ranar Kyari zai kama aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.