Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo- Rikici

Rikicin kabilanci ya tilastawa mutane dubu 300 tserewa a Congo

Sama da mutane dubu 300 ne suka tsere daga gidajensu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a makonni biyu da suka wuce, sakamakon rikicin kabilanci da ya lakume fiye da rayuka 50 a wasu yankunan kasar.

Wasu al'ummar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo
Wasu al'ummar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo AFP
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwa game da barkewar rikicin a yankin Ituri a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda ta ce ta ga hare–hare da dama a tsakanin al’ummar kabilar Hema da Lendu.

Mai magana da yawun Hukumar, Babar Baloch, ya shaida wa manema labarai cewa sama da mutane dubu 300 ne rikicin ya tilasta wa barin gidanjensu, yana mai bayyana fargabar cewa yaduwar rikicin na iya shafar da dama daga sassan yankin.

Shi ko gwamnan yankin Ituri, Jean Bamanisa Saidi, shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa ya yi cewa, adadin wadanda rikikcin ya daidaita na iya zarce dubu 400.

A makon da ya gabata, jami’ai a yankin sun bayyana cewa, adadin wadanda aka kashe a rikicin ya kai akalla 50, yayin da wasu majiyoyi na dabam suka ce wadanda suka mutu sun zarce 70.

Ya zuwa yanzu ba a san dalilin rikici da ya lakume rayuka tare da daidaita mutane da dama ba, amma rikicin ya faru ne a yankin da dubun dubatan mutane suka mutu a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003, lokacin da kabilar Hema da na Lendu suka baiwa hammata iska.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.