Isa ga babban shafi
Afrika-Kaciyar mata

Matan da suka fuskanci kaciya sun koka da halin da su ke ciki a Afrika

Matan da suka tsira daga kaciyar da ake musu a Afirka sun bukaci taimakon gwamnatocin kasashen su domin shawo kan matsalar yanayin da suka samu kan su da ke da nasaba da fitar hankali.

Wasu mata da suka yi zaman dirshan a tsakiyar birnin Dhakar na Senegal
Wasu mata da suka yi zaman dirshan a tsakiyar birnin Dhakar na Senegal RFI/William De Lesseux
Talla

Irin wadannan matan da suka fuskanci irin wannan kaciya da kuma masu kare muradun su a nahiyar Afirka sun bayyana halin da suka samu kan su ne wajen wani taro a kasar Senegal kan yadda kaciyar ke sa wasu daga cikin su samun tabin hankali.

Ita dai kaciyar wanda ake danganta ta da addini da kuma al’ada daga kabila zuwa kabila ana gudanar da ita ne a kasashe 28 na Afirka, matakin da ke yin illa ga mata ciki har da hana su haihuwa ko kuma kai wa ga mutuwar su.

Virginia Lekumosia, wata da ta tsira daga kaciyar a Kenya, ta ce babu isassun asibitocin da ke kula da matan da suka fuskanci irin wannan matsala a Afirka.

Aida Ndiaye, wata yar kasar Senegal ta ce ba ta yi rashin nasarar samun illa ba lokacin da aka mata kaciyar ta na da shekaru 6, amma har yanzu tana tuna ukubar da ta shiga.

Shugabannin kasashen duniya a shekarar 2015 sun yi alkawarin haramta kaciyar baki daya.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana da karancin likitocin da ke kula da masu fama da tabin hankali a Afirka, inda likita guda ke duba mutane 100,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.