Isa ga babban shafi
Najeriya-Adamawa

Gwamnatin Adamawa ta tabbatar da barkewar cutar kwalara a sassan jihar

Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da bullar annobar cutar Amai da gudawa a wasu sassan jihar bayan samun akalla mutane 76 da suka kamu da cutar yayinda wani guda kuma ya mutu.

Wasu masu fama da cutar kwalara a Najeriya
Wasu masu fama da cutar kwalara a Najeriya NAN
Talla

Cikin sanarwar da ma’aikatar lafiyar jihar ta Adamawa ta fitar yau Talata, ta bukaci al’umma da su dauki matakan tsabtace muhallansu baya ga gaggauta ziyartar asibitoci da zarar an fuskanci alamomin cutar.

Rahotanni sun bayyana cewa tun a ranar 12 ga watan Mayun da ya gabata ne aka fara fuskantar annobar cutar ta Amai da gudawa a yankunan kananan hukumomin Yola ta arewa da Yola ta kudu da kuma Girei.

Ma’aikatar lafiyar ta Adamawa ta bayyana cewa, sai da ta gudanar da dogon bincike da gwaje-gwaje kan wadanda suka kamu da cutar tukuna ta gano cewa annoba ce ta kwalara, kuma tuni ta fara daukar matakan gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.