Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Super Falcons ta Najeriya ta fita daga gasar cin kofin duniya

Super Falcons ta Najeriya ta sha kashi a hannun takwararta Les Bleus ta Faransa da ci daya mai ban haushi, a wasan karshe na cikin rukuni, a gasar cin kofin duniya ta mata da ke ci gaba da gudana a Faransar.

'Yan wasan tawagar kwallon kafar Super Falcons ta Najeriya
'Yan wasan tawagar kwallon kafar Super Falcons ta Najeriya Pulse.ng
Talla

Super Falcons ta Najeriya ta sha kashi a hannun takwararta Les Bleus ta Faransa da ci daya mai ban haushi, a wasan karshe na cikin rukuni, a gasar cin kofin duniya ta mata da ke ci gaba da gudana a Faransar.

Wasan wanda ya gudana a filin wasa na Roazhon Park mai daukar ‘yan kallo dubu 28 da ke birnin Rennes, ya samu halartar ‘yan kallo da magoya bayan bangarorin biyu, wadanda suka cika filin wasan.

Sai da aka shafe sama da mintuna 70 ana dauki ba dadi kafin Faransa ta saka kwallo a ragar Najeriya, bayan ta samu bugun daga – kai – sai –mai tsaron – raga, inda ‘yar wasan Faransa, Wendy Renard ta buga, ta kuma saka kwallon a ragar Najeriya.

Sai dai wannan bugun daga – sai – tsaron – raga ya janyo cece kuce, ganin cewa Renard ba ta saka kwallon a raga ba tun da farko, sakamakon fita waje da kwallon ta yi, amma sai alkalin wasa ta sa aka maimaita bugun, wai saboda mai tsaron ragar Najeriya ta motsa kafin a buga kwallon.

Yanzu haka Faransa ta fito a ta daya a rukuni na daya,yayin da Norway da ta doke Koriya daci 2 da 1 adaya wasan ta kammala matakin rukuni a matsayi na biyu; da haka, dukkanninsu sun samu tsallakawa zuwa matakin kungiyoyi 16 kenan, Super Falcons ta Najeriya kuwa sai haramar dawowa gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.