Isa ga babban shafi
Uganda

Bobi Wine (mawaki kuma dan adawar Uganda): « ina kiran juyin juya hali ta ruwan sanyi»

A karas Uganda wani dan majalisar dokoki da ake kira «Honorabl Robert Kyagulanyi». Sai dai mafi yawan yan kasar sun fi saninsa da sunansa na mawaki: Bobi Wine. Shi ne kuma bakonmu a yau, a wani bangaren kuma dan adawa ne ga sugaba Museveni, haka kuma mawaki zamani na salon kidan Afrika da ake kira Afrobeat da kuma reggae. Gwagwarmayar siyasarsa ta kasance masa mai tsadar gaske. An haramta saka wakokinsa a gidajen radiyo da Talabijin, haka kuma, idan bai kasance a gida tsare ba, to kuwa mawakin na karakaina a kotu. A watan Afrilun da ya gabata, an kama shi, tare kuma da zarginsa da laifin tsara wani taron gangami ba da izni ba a 2018. Bayan da ya share kwanaki uku a tsare, an sallame shi kan beli. A ziyarar da yake yi yanzu haka a nahiyar turai, Bobi Wine ya gabatar da wakoki a kasashen Danemark da Pays-Bas ko Netherland, inda nan gaba zai gabatar da wakoki a kasashen Swidin da Jamus. A kan hanyarsa da ta kawoshi a birnin Paris ya karba wasu tambayoyi daga Radiyo Faransa Internationale RFI.

mawaki Bobi Wine daya daga cikin yan adawar shugaba Museweni na Uganda (anan gaban wata kotu a kampala a watan Afrilu 2019).
mawaki Bobi Wine daya daga cikin yan adawar shugaba Museweni na Uganda (anan gaban wata kotu a kampala a watan Afrilu 2019). Nicholas BAMULANZEKI/AFP
Talla

RFI: Ina kwana, da wane suna kake bukatar a kira ka, Bobi Wine ko Robert Kyagulanyi ?

Bobi Wine: Na fi son in saukaka, jama’a su kira ni da sunan da suke so, bukata ta dai ita ce su fahimci sakona.

Wane ne sakon ?

Sakon yanci, da yantarwa, musaman domin al’umma su iya kai inda ake bukata

A cikin wakokinka kana sukar shugaba Museveni kana danganta mulkinsa « da mulkin Soja». Hakikance me kake zarginsa da shi ?

shugaban Museveni na kan mulki yau da shekaru 33. Ya zo kan karagar mulki ta hanyar karfin makamai, da kuma mulkin fir’aunancinsa domin ci gba da mulki ta hanyar nuna karfin makamai, duk wanda kuma ya nuna adawa e à Museveni, shugaban rai da rai za a far masa a kuma lalata shi.

Ya kamata a sani shugaba Museveni ya fufe bakunan yan adawarsa. Ya kamasu ya rufesu a kurkuku, da dama daga cikinsu an kashe su.

Abin da ni da abukanaina muka runguma juyin juya hali ne na matasa, juyin juya hali a cikin ruwan sanyi. Muna bukatar hada kan dukkanin yan kasar Uganda da suka gaji damulkin fir’aunanci na soja, domin karbar abindake nasu : yanci, demkradiya da kuma doka da oda.

Muna bukatar son ganin karshen mulkin soja domin yan uganda su samu damar cin gajiyar yancinsu a matsayinsu na yan kasa.

Don me kake danganta gwamnatinsa da ta Soja ? Al halin kuwa zaben sa aka yi…

Mun lura da cewa albarkacin wanna zabe, shugaba Museveni na tura sojoji kan jama’a suna dukarsu, kuma yana shiraya a ringizon kuri’a a zabubbukan. A zaben shugabancin kasar da ya gabata na 2016 sojoji sun mamaye rumfunan zabe, haka kuma manyan yan takarar adawa irinsu, Kizza Bessigye, an kamasu an tsare su a cikin gidajensu, tare ma da hanasu zuwa kotu.

Duk wannan aiki ne na shugaba Museveni. A kasashen ketare kuma yana gabatar da kansa a matsayin dan demkradiya. Shine dalilin da ya sa mutane da dama ke ce masa dan mulkin kama karya ne na hakika. Amma ya kamata a sani wakokina an haramta su, bani da yancin halartar duk wani taron gangamin al’umma, don kawai na soki shugaba Museveni – domin kawai ni da magoya bayana mun bayyana aniyarmu ta tsayawa zaben nemen kujerar shugabancin kasa.

A Uganda, ayyana son tsaya wa neman zaben kujerar shugabancin kasa laifi ne.

Kana bukatar tsayawa neman kujerar shugabancin kasar Uganda ?

Kwarai, na fade shi na kuma sake nanatawa. Ni da magoya bayana da gaske muna bukatar kalubalantar shugaba Museveni a zabe mai zuwa. Kasa da shekaru biyu masu zuwa. Kar a yi mamaki idan a madadin magoya bayana na tsaya takara, idan har magoya bayan nawa sun amince da haka.

Saboda wane dalili ne mawaki kamar ka ke bukatar tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasa?

Ina wakiltar matasa masu tasowa ne. Ina kuma wakiltar wadanda aka manta dasu ne, mazauna unguwanin bayan gari. Akwai talakawa da dama a Uganda. Sama da kashi 80% na al’ummar kasar na rayuwa ne a cikin talauci. Wanda ni da abukaina muke karewa, wani tunani ne na juyin juya hali : tunani da ya kamata mutanen kwarai su goyi bayansa ta hanyar nuna kishin kasa da zuciya guda.

Ba zamu kuma fasa nanata cewa: Ugnda ta yan kasa ce, ba ta shugaba Museveni da iyalansa ba.

Ana kokarin kafa wani hadin gyuiwar yan adawa, yaushe ne wannan hadin gyuiwa zai tabbata?

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin daukacin jam’iyun dake bukatar samun sauyi. Mun sani cewa, a lokutan da suka gabata mun kasa magance rarrabuwar kanunmu na siyasa da zamnatakewa, da ya rarraba jam’iyun siyasarmu, da kuma na fararen hula, yanzu kuma a Uganda an kasa biyune, tsakanin masu gallazawa da wadanda ake gallazawa. Idan Allah ya so zamu cimma nasarar gabatar da dan takara yan adawa guda daya. Wannan kuma, za a sanar da shi nan bada dadewa ba.

An samu bulluwar annobar cutar Ebola ta farko a Uganda. Ta hanyar wani karamin yaro dan kasar Congo mai shekaru 5. Me ya kamata Uganda ta yi?

Karamci wani abu ne da ke da matukar muhimmanci a cikin zukata, da kuma ake kokarin martabawa a Uganda. Wannan wani hali ne na al’ummarmu. Duk da haka ya kamata ma’aikatun kiyon lafiyarmu su kara daukar matakan taka tsantsan. Ba a karo na farko ba ne aka samu bulluwar annobar Ebola. Ya kamata a kara bada himma a cibiyoyin kiyon lafiya domin killacewa, da kuma yakar annobar.

Ya kamata a refe kan iyakar?

Bai dace ba ! ba zamu iya kin karba makwabcin da gidansa ke cin wuta ba. Sam, mun yarda da nuna karamci da yan uwantaka. Idan har an samu bulluwar annoba daga wancan bangaren na ketaren iyaka, ya kamata mu kai dauki da yan uwanmu maza da mata.

Kasar Botswana ta dage haramcin auren jinsi guda, kana ganin ya kamata Uganda ta yi irin wannan?

Yancin dan adam yancindan adam ne tun daga Faransa har zuwa Afrika. Dukkanmu yanci guda muke dashi.

A lokutan da suka gabata wakokinka na kyamar auren jinsi…

Gaskiya ne. Amma kamar yadda kuka fada, a lokuttn da suka gabata ne. A hannan lokaci kuma ina sukar siyasar yan siyasa ne kuma, daga karshe na fahimci cewa duk siyasa ce. A kan haka ina mutunta kowa a yau, har da wadanda bamu hada ra’ayi da tunani iri guda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.