Isa ga babban shafi
kamaru

kamaru ba zata lamunci katsalandan a kokarin sasanta rikicinta da yan aware ba

A gaban wani taron jikadun kasashen ketare a Yaounde, ministan harakokin waje da hulda na kasar Kamaru Lejeune Mbella Mbella, ya bayyana aniyar gwamnatin kasar na son kawo karshen rikicin siyasa da na zamantakewa a yankin dake amfani da turancin Inglishi. sai dai ya yi watsi da duk wani shiga tsakanin wata kasa ta ketare a cikin lamarin.Ministan dake kula da hulda da kasashen na ketare Lejeune Mbella Mbella ya bayyana hanyoyin da suke bi yanzu haka wajen tabbatar da magance matsalar yan awaren yankunan 2 dake fama da tashe tashen hankullaa kasar.

shugaban Kamaru Paule Biya
shugaban Kamaru Paule Biya © AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

A gaban jikadun kasashen ketaren, Lejeune Mbella Mbella, ya tabbatar da cewa matakin soja da ake dauka yanzu haka ba zai taimaki gwamnati ba, face shiga tattaunawa kai tsaye inda ya ce, tuni gwamnati ke cikin tattaunawar tun farkon barkewar rikicin.

A lokacin da yake kare sojojin kasar da sau tari aka nuna da yatsa kan take hakkin dan adam a wadannan yankuna biyu masu fama da tashin hankali. Ministan Ya bayyana mamakin gwamnatinsa ta hanyar nanata cewa, aikin jami’an tsaron da aka tura a fagen daga shine tabbatar da bin doka da oda, tabbatar da kasar ta ci gaba da zama dunkullaliya, tare kuma da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu kuma shi suke yi, A gaban yan awaren da kuma yan ta’addan da manufarsu ita ce ta raba kasar Kamaru tare da son kifar da gwamnatinta

A ya yinda yake jawabi cikin kakkausan harshe jikadan Kamaru a Faransa ya tabbatar da abinda ke faruwa a yankunan arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin kasar ta kamaru, da zama abin damuwa, sai dai kuma a cewarsa ba mai haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaron kasashen duniya ba ne.

Furucin dake nuni da cewa, matsin lambar da da kasashen duniya ke yi ba zai sa gwamnatin, Yaoundé ta saki baki a zana mata hanyoyin warware rikicinba.

Alhalin masalahar ta yayan kasar Kamaru ce, a dai dai lokaci da ake cigaba da daga muryar neman shiga tsakanin kasashen duniya wajen warware takadamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.