Isa ga babban shafi
Faransa-Sahel

Faransa ta ce bai kamata ba kasashen Sahel su dogara da ita wajen tsaron kansu ba.

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean – Yves Le Drian, ya shaida wa kasashen yankin Afirka ta Yamma da ke yaki da ‘yan ta’adda da kada su shagala da kasancewar dakarun Faransa a yankin, saboda ba zaman dindindin suke ba.

Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian
Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Yankin na Sahel na fama ne da karuwar rikici da hare hare daga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke da alaka da al Qaeda da kuma kungiyar IS, abin da ke nuni da mayuwacin halin da abokai na kasashen duniya ke fuskanta wajen kawo zaman lafiya a yankin.

Yankin arewacin Burkina Faso da ke da iyaka da Mali da Nijar, ya sha ruwan hare hare a ‘yan watannin baya, yayin da rikice rikicen kabilanci da ke ci gaba da ta’azzara ya dada dagula al’amura.

Le Drian ya ce, bai kamata gwamnatocin kasashen yakin Sahel su saki jiki suna tunanin cewa dakarun Faransa na tare da su ba, su ya kamata su tabbatar da tsaronsu, don ba zaman har abadan abadin dakarun Faransa ke yi a yankin ba.

Faransa, wacce ita ta yi wa kasashen yankin Sahel mulkin mallaka, ta kawo dauki Mali a shekarar 2013 don korar mayakan jihadi da suka mamaye arewacin kasar. Tun daga wannan lokacin ta jibge dakarunta 4500 da sunan yaki da ta’addanci.

A karkashin jagorancin Faransa, kasashen yammacin Turai na samar da kudaden tafiyar da dakarun yankin da suka kunshi sojoji daga Mali, Nijar, Burkina Faso, Chad da Mauritania don fatattakar ‘yan ta’adda, amma tsaikon da ake samu na isar kudin ga dakarun tsakanin kasashen 5 yana kawo koma baya yayin da rikicin ke ta’azzara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.