Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia: Kotu ta yanke hukunci kan sojin da sukai yunkurin juyin mulki

Kotun sojan Gambia ta yankewa wasu dakarun kasar 8 hukunci bayan samunsu da laifin shirya yiwa shugaban kasar Adama Barrow juyin mulki a shekarar 2017.

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh tare da matarsa Zineb, yayin shirin kada kuri'a, a birnin Banjul, yayin zaben shugabancin kasar. 1/12/2016.
Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh tare da matarsa Zineb, yayin shirin kada kuri'a, a birnin Banjul, yayin zaben shugabancin kasar. 1/12/2016. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Kotun sojin ta ce shaidu kwarara sun nuna cewa, jami’an sojin da aka yankewa hukunci sun shirya aiwatar da juyin mulkin tare da taimakon tsohon shugaban kasar ta Gambia Yahya Jammeh, da ya shafe shekaru 22 yana mulki.

A shekarar 2016 shugabancin Jammeh ya zo karshe, bayan kayen da yasha a hannun Adama Barrow a zaben shugabancin kasar.

A waccan lokacin dai Jammeh ya ki sauka daga mulki, har sai da ya fuskanci matsin lamba daga kasashe a ciki da wajen nahiyar Afrikakafin ya bada kai bori ya hau.

An dai tuhumi sojojin kasar ta Gambia 8 ne da suka shafi yunkurin juyin mulkin, wadanda suka hada da, cin amanar kasa, da kuma shirin cake ilahirin ministocin Adama Barrow, sai kuma shirya kai farmaki kan rundunar soji ta kasa da kasa da ke kasar ta Gambia.

Daga karshe kotun sojin ta yankewa 7 daga cikin sojojin hukuncin daurin shekaru 9, yayinda za a daure guda tsawon shekaru 3.

Shaidun da kotu ta yi amfani da su, sun tabbatar da cewa masu laifin sun yi musayar bayanai tsakaninsu da tsohon shugaba Yahya Jammeh ta kafar WhatsApp kan shirin aiwatar da juyin mulkin ga gwamnatin Adama Barrow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.