Isa ga babban shafi

Mutane 30 sun mutu a Congo sakamakon kifewar kwale - kwale

Akalla mutane 30 ne suka mutu yayin da da dama suka jikkata, sannan karin wasu suka bace, bayan hatsarin kwale kwale a wani tafki dake yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi REUTERS/ Olivia Acland
Talla

Magajin garin yankin, Simon Mbo Wemba ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa cikin gawarwaki 30 da aka tsamo daga tafkin, akwai mata 12 da yara 11 da maza 7.

Ya kara da cewa kwale-kwalen na dauke da fasinjoji 350 ne, kuma daga cikinsu 180 ne suka tsira daga hatsarin da ya auku a tafkin na Ndombe.

Magajin garin ya ce har yanzu dai ana sa rangano karin gawarewaki, yana mai nuni da cewa zai yi matukar wahala a tantance wadanda hatsarin ya rutsa da su saboda yawancin fasinjojin kwale - kwalen na iya zama bakin haure.

Sufuri ta ruwa na daya daga cikin hanyoyin sufurin da aka fi amfani da su a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da ke da hanyoyin ruwa da yawa, amma ana yawan samun hastari, wadda diban fasinjoji fiye da kima ke haddasawa.

Ko a watan da ya gabata, mutane 167 ne suka mutu a wani hatsarin kwale - kwale, lamarin da ya sa shugaba Felix Tshisekide wajibta wa duk wani fasinja sanya falmarar ruwa yayin tafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.