Isa ga babban shafi
Najeriya-CHAD

Boko Haram ta kashe sojojin Chadi da Najeriya

Akalla sojojin Chadi hudu da na Najeriya uku sun rasa rayukansu a wasu mabanbantan hare-haren da kungiyar Boko Haram da kaddamar musu. 

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram pmnewsnigeria
Talla

Boko Haram ta kashe sojin Chadi da wani dan jarida mai daukar hoto a harin da ta kai musu a wani sansani da ke yankin arewacin tafkin Chadi

Sai dai bayanai na cewa, sojojin na Chadi sun yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram 23.

Sojin Najeriya kuwa sun rasa rayukansu ne a harin da kungiyar ta kai musu a sansanin garin Gubio mai tazarar kilomita 80 daga babban birnin Maiduguri na jihar Borno.

Maharan sun kai farmakin ne da yammacin jiya Asabar, inda suka yi lugudan wuta tare da fatattakar sojojin na Najeriya.

Rahotanni na cewa, har yanzu akwai sojoji guda shida da suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.