Sudan za ta tsunduma yajin aikin gama-gari saboda mulki
Jagororin masu zanga-zanga a Sudan sun bukaci gudanar da yajin aikin gama-gari na tsawon kwanaki biyu wadda za a fara a ranar Talata mai zuwa biyo bayan gaza cimma matsaya tsakaninsu da sojojin kasar dangane da kafa mulkin farar hula a kasar.
Wallafawa ranar:
An jingine tattaunawa tsakanin bangarorin biyu tun a ranar Litinin da ta gabata sakamakon yadda suka samu banbancin ra’ayi kan wanda zai jagoranci sabuwar gwamnatin kasar.
Jagororin zanga-zangar sun ce, a yanzu babu wani zabi da ya wuce tsunduma cikin yajin aikin gama-gari kamar yadda sanarwar da suka fitar ke cewa.
Yajin aikin dai zai shafi cibiyoyin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu a cewar masu zanga-zangar da suka yi nasarar ganin bayan mulkin Omar al-Bashir.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu