Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

An rantsar da Cyril Ramaphosa a wani sabon wa'adin shugabancin Afrika ta Kudu

Cyril Ramaphosa a wani sabon wa’adi na shugabancin kasar ya karbi rantsuwar kama aiki a Pretoria.Shugaban kasar a lokacin da yake karbar rantsuwar ya dau alkawali na inganta rayuwar al’umma da kuma samar da daidaito tsakanin jama’a tareda mayar da kasar saman turbar tattalin arziki.

Cyril Ramaphosa Shugaban Afrika ta kudu a lokacin karbar rantsuwa a Pretoria
Cyril Ramaphosa Shugaban Afrika ta kudu a lokacin karbar rantsuwa a Pretoria REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Shugaban kasar Cyril Ramaphosa mai shekaru 66 ya sake samun goyan bayan yan majalisun kasar ne ranar laraba da ta gabata,yan Majalisun jam’iyyar ANC mai mulki da suka samu rijaye a zaben kasar na ranar 8 ga wannan watan da muke cikin sa.

Sai dai tsohon Shugaban kasar Jacob Zuma bai halarci rantsar da Shugaban kasar bisa wasu dalilai da suka shafi kotu kamar dai yada ya sanar .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.