Isa ga babban shafi
Kenya

Kotun Kenya ta amince da dokar haramta luwadi

Babbar Kotun Kenya ta ki soke dokar da ke haramta luwadi da madigo a kasar, matakain da ake kallo a matsayin gagarumin koma-baya ga masu wannan dabi’ar.

Alkalan Kotun da ke Nairobi sun amince da dokar haramta madigo da luwadi a Kenya
Alkalan Kotun da ke Nairobi sun amince da dokar haramta madigo da luwadi a Kenya REUTERS/Baz Ratner
Talla

Kungiyoyin Kare Hakkin ‘Yan Luwadi da suka shigar da kara shekaru uku da suka gabata a gaban kotun, sun yi fatan cewa, kasar ta kenya za ta bi sahun kasashe irinsu Angola da India wajen kawo karshen dokar haramta luwadin.

Sai dai Kotun ta ce, dokar haramcin bata saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba, yayinda ta yi la’akari da al’adun gargajiyar da kasar ta gada.

Jim kadan da yanke wannan hukuncin, masu luwadi da madigo suka fashe da kuka a harabar kotun, tare rungumar juna da kuma sharewa juna hawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.