Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta bayyana Dr Bello Mutawalle zababben Gwamnan Jihar Zamfara

Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana Dr Bello Mutawalle na Jam’iyyar PDP a matsayin zababben Gwamnan Jihar Zamfara, sakamakon korar Yan takarar Jam’iyyar APC da kotun koli tayi jiya, saboda abinda ta kira rashin gudanar da zaben fidda gwani a matakai daban daban.

Tutar jam'iyyar mai adawa a Najeriya PDP
Tutar jam'iyyar mai adawa a Najeriya PDP premiumtimes
Talla

Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana Mutawalle a matsayin zababben Gwamna saboda shi ya zo na biyu a yawan kuri’u a zaben da akayi a watan Maris da ya gabata.

Farfesa Yakubu yace Mutawalle ya cika duk sharuddan da ake bukata, saboda haka shine zababben Gwamna da za’a baiwa takardar shaida ranar litinin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.