Gwamnonin Najeriya sun bijirewa 'yancin kananan hukumomi
Gwamnonin Najeriya sun bayyana adawar su da aniyar hukumar yaki da halarta kudaden haram ta NFIU wadda ta haramta mu su taba kudaden kananan hukumomi daga ranar 1 ga watan Yuni mai kamawa.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwar da suka rabawa manema labarai, Gwamnonin sun ce sun rubuta wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya sanya baki cikin lamarin wanda ke dauke da sanya hannun shugabansu Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari.
Gwamnonin sun bayyana cewar yunkurin wannan hukuma ta NFIU ya sabawa dokokin kasa wanda suka dora alhakin kula da kananan hukumomi a hannun gwamnatin jihohi.
Wasikar da Gwamnonin suka rubuta ta zargi wannan hukuma da kokarin bata musu suna da kuma wuce makadi da rawa wajen gudanar da aikin ta.
A baya duk wani yunkuri na yantar da kananan hukumomi da kuma sake musu mara na samu nakasu daga gwamnonin jihohi wadanda ke da karfin fada aji fiye da kima a siyasar Najeriya.
Yunkurin sauya kundin tsarin mulki da zummar yantar da kananan hukumomin yaci tura, ganin yadda gwamnonin suka tirsasawa majalisun jihohi wajen kin amincewa da shiri bayan majalisar wakilai da ta dattijai sun goyi bayan sa.
Ita dai hukumar NFIU tayi gargadin cewar duk wani jami’in gwamnati ko banki ko wata cibiyar kudade da ta kuskura ta taba kudaden hukumomi daga ranar 1 ga watan Yuni zata fuskanci fushin hukuma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu