Bakonmu a Yau
Farfesa Tijjani Muhammad Naniya kan matakin gwamnatin Kano na raba masarautar jihar zuwa gida 4
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:38
Majalisar Dokokin Kano, ya kada kuri’ar amincewa dokar kafa ma’aikatar kula da Mulki da Masarautun Gargajiya, matakin da ya bada damar aiwatar da kudurin nada sabbin Sarakunan Yanka guda hudu a jihar ta Kano.Garuruwan da gwamnatin Kano za ta nada sabbin Sarakunan masu daraja ta daya sun hada da Gaya, Karaye, Bichi da kuma Rano. Dangane da wannan ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Tijjani Muhd Naniya masanin Tarihi da ke Jami’ar Bayero.