Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/11 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/11 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 22/11 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 22/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 22/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Hukumar Lafiya ta damu kan kisan da Ebola ke yi

media Wannan dai ne karo na 10 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar annobar cutar ta Ebola REUTERS/Baz Ratner

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta nuna fargaba kan karuwar mutanen da su ke mutuwa sandiyyar annobar cutar Ebola a Jamhuriyyar Demokradiyyar bayan mutuwar wani jariri mai watanni 9 da haihuwa.

A cewar hukumar wadda ta fara tunanin sauya maganin rigakafin cutar da ake amfani da shi yanzu haka a kasar ta Congo, adadin wadanda cutar ta hallaka ya kai 994 yayinda zai iya cikewa dubu guda kowanne lokaci daga yanzu.

Hukumar ta WHO ta ce za ta sauya maganin da ta fara amfani da shi na Merck a matsayin rigakafi zuwa wani nau’in magani da kamfanin magani Johnson & Johnson, zai samar.

Sai dai babban dakaraktan hukumar ta WHO Dr Michael Ryan, ya ce akwai yiwuwar a hada magungunan biyu don gaggauta kawar da cutar ta Ebola, da ke cigaba haddasa asarar rayuka a kasar.

A wani taron manema labarai da ya kira a Geneve, Dr Ryan yanzu haka akwai mutane dubu 12 da ke zaman jiran magungunan cutar ta Ebola, dai dai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da barazana ga aikin agaji a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Wannan dai ne karo na 10 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar barkewar cutar ta Ebola wanda a kowanne lokaci kuma kan hallaka tarin tarin jama'a.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure