Conde na fuskantar turjiya kan sauya kudin tsarin mulki
Magoya bayan shugaban kasar Guinea Alpha Conde da masu adawa da shi, sun yi arangama da juna a jiya talata, abinda yayi sanadin jikkata wasu da dama, sakamakon bukatar shugaban na sauya kundin tsarin mulki domin yin wa’adi na uku.
Wallafawa ranar:
Shugaba Conde mai shekaru 81, shi ne zababben shugaban Guniea na farko da aka zaba a shekarar 2010, kafin daga bisani ya sake lashe wa’adi na biyu shekaru 5 da suka gabata.
Kundin tsarin mulkin kasar ya halasta wa’adi biyu ne, tsarin da shugaba Conde ya dade yana kalubalanta.
Bangaren Adawa a kasar ta Guinea ta kalubalanci matakin masu dafawa Shugaban kasar na mika wuya don Alpha Conde ya cigaba da mulkin kasar a wasu shekaru biyar nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu