Isa ga babban shafi
Sudan

An yi zanga-zangar tilasta wa sojoji a Sudan

Dubun-dubatar mutane ne suka halarci zanga-zangar da aka gudanar a birnin Khartoum na kasar Sudan sakamakon kiran da ‘yan adawa suka yi wa jama’a don tilasta wa sojoji gaggauta mika ragamar mulki a hannun fararar hula.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar a Sudan
Wasu daga cikin masu zanga-zangar a Sudan REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Kawancen samar da ‘yanci da kuma sauyi a Sudan, wanda ya kunshi kungiyoyi da jam’iyyun siyasar da ke adawa da mulkin hambararren shugaba Omar al-Bashir ne ya bukaci a gudanar da wannan gangami da aka yi hasashen cewa, zai tara mutane milyan daya a daidai lokacin da sojojin ke cewa a shirye suke su saurari bukatun al’umma.

Mutane, wasu a cikin manyan motoci wasu kuwa a cikin jirgin kasa daga sassa daban daban na kasar ne suka halarci zanga-zangar, wadda aka shirya kwana daya bayan da uku daga cikin manyan kusoshi a Majalisar Mulkin Sojojin kasar suka yi marabus daga mukamansu, sakamakon cijewar tattaunawar da aka fara dangane da batun kafa sabuwar gwamnatin riko a kasar.

Mahalarta wannan gangami sun rika rera taken cewa ‘’mulkin farar hula muke bukata’’, yayin da wasu ke cewa ‘’mun fito ne domin kare nasarar juyin juya halin da ya yi awon gaba da mulkin al-Bashir’’

Alkalai da dama a cikin bakaken tufafinsu ne suka yi tattaki daga ginin kotun kare tsarin mulkin kasar zuwa ake gudanar da gangamin, kuma a cewarsu sun fito ne domin tabbatar da ‘yancin bangaren shari’a da kuma hana ‘yan siyasa yi masu shishigi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.