Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai jagoranci taron farfado da Tafkin Chadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da bukatar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na jagorancin wani taron kaddamar da gidauniyar tara Dala biliyan 50 da za ayi amfani da shi wajen farfado da tafkin Chadi da ke ci gaba da tsukewa.

Shugaba Muhammadu Buhari da  Akinwumi Adeshina
Shugaba Muhammadu Buhari da Akinwumi Adeshina Bashir
Talla

Yayin da yake karbar bukatar Guterres ta hannun shugaban Bankin raya Kasashen Afrika, Dr. Akinwumi Adeshina, shugaba Buhari ya yaba da matakin wanda ya ce, zai bada damar sake samarwa mutanen da ke kewayen tafkin ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

Daga bisani shugaban kasar ya yaba da jagorancin Adeshina a Bankin Afrika, wanda ya ce, ya bada gudumawa wajen samar da ci gaba da dama a nahiyar Afirka.

Dr. Adeshina ya shaida wa shugaba Buhari cewar, Bankin ya samu nasarori da dama musamman wajen inganta harkokin noma da kasuwanci da kuma gina kayan more rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.