Isa ga babban shafi
Masar- AU

Shugabannin Afrika za su gana kan Sudan da Libya

Kasar Masar za ta karbi bakwancin taron Kungiyar Kasashen Afrika na gaggawa domin tattaunawa kan rikice-rikicen da suka taso a kasashen Libya da Sudan.Taron na gobe Talata zai samu halartar wasu shugabannin kasashen da ke nahiyar.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika
Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Fadar shugaban kasar Masar, Abdel Fatah al-Sisi da ke shugabancin kungiyar ta AU, ta ce, shugabannin da za su halarci taron za su mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a Sudan, in da ake ci gaba da samun zanga-zanga bayan sojoji sun kifar da gwamnatin shugaba Omar Hassan al-Bashir.

Taron zai kuma duba yadda za a kawo karshen tashin hankalin da ake ci gaba da fama da shi a Libya wanda ke ci gaa da haddasa asarar rayuka tsakanin dakarun Janar Khalifa Haftar da sojojin gwamnati.

Daga cikin shugabannin da ake saran za su halarta har da shugaban Chadi, Idris Deby da shugaban Rwanda, Paul Kagame da na Congo, Dennis Sassou Nguesso da na Somalia, Mohammed Abdullahi Mohammed da na Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa da kuma Isma’il Guelleh na Djibouti.

Ana saran wakilan kasashen Habasha da Sudan ta Kudu da Najeriya tare da shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afrika, Mousa Fakki Mahamat su halarci taron.

Wannan taron shi ne zai zama na farko da shugabannin kasashen Afrika za su gudanar kan rikice-rikcen da suka dabaibaye wadannan kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.