Shugaban sashen fikira na Sudan ya yi murabus
Shugaban sashen fikira na Sudan ya sanar da ajje mukaminsa yau asabar kwana guda bayan shugaban rikon kwaryar da ya maye gurbin shugaba Omar al-Bashir ya yi murabus sakamakon ci gaban zanga-zanga a kasar ta neman mulkin farar hula ba soji ba.
Wallafawa ranar:
Salah Abdallah Mohammed Saleh, wanda aka fi sani da Salah Gosh, shi ne mutum na biyu mai karfin fada aji a kasar bayan Omar al-Bashir, kuma shi ne ake zargi da umarnin duk kisan da jami’an tsaro suka yi lokacin zanga-zangar kasar ta fiye da watanni 4.
Tuni dai shugaban hukumar tsaro na kasar ta Sudan Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan ya karbi murabus din Salah Gosh.
Yanzu haka dai al'ummar Sudan na ci gaba da bore kan lallai a samar musu da gwamnatin farar hula sabanin mulkin soji da sashen tsaron kasar ke kokarin yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu