Isa ga babban shafi
Sudan

Sabon shugaban mulki Soji na Sudan zai kafa gwamnatin farar hula

Sabuwar gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Soji a Sudan ta yi alkawarin samar da gwamnatin farar hula cikin kasa da shekaru biyu, bayan tattaunawa da bangaren gwamnati mai barin gado da kuma jagororin adawar kasar, dai dai lokacin da masu zanga-zanga ke ci gaba da boren matakin.

Dandazon jama'ar Sudan da ke bore kan neman lallai gwamnatin sojin kasar ta kafa mulkin farar hula
Dandazon jama'ar Sudan da ke bore kan neman lallai gwamnatin sojin kasar ta kafa mulkin farar hula AFP
Talla

Cikin wani jawabin kai tsaye ta gidan Talabijin din kasar karon farko da ya gabatar Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan Abdelrahman da ke matsayin shugaba a yanzu, ya ce ya janye dokar haramta zirga-zirgar cikin dare, haka zalika ya yi umarnin sakin ilahirin fursunonin siyasa da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al Bashir ta daure.

Bayan nasarar soji ta Hambarar da gwamnatin al Bashir a shekaran jiya Alhamis, a daren jiya Juma’a ministan tsaron kasar Awad Ibn Auf da tun farko ya dare kujerar shugabancin kasar ya yi murabus, haka zalika Salah Abdallah Mohemmed Saleh, shugaban sashen fikira na kasar, wanda ake zargi da umarnin kashe-kashen da ya faru yayin zanga-zangar watanni 4 da ta gudana a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.