Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana fargabar rasa rayuka a sabon rikicin Tibi da Jukun a Taraba

Mutane da dama ake fargabar sun rasa rayukansu a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun a yankin Wukari na Jihar Taraba da ke arewacin Najeriya.

Ko a shekaran jiya Alhamis makamancin rikicin ya hallaka mutane 12 a jihar ta Taraba
Ko a shekaran jiya Alhamis makamancin rikicin ya hallaka mutane 12 a jihar ta Taraba
Talla

Wasu ganau da suka gujewa rikicin a kudancin jihar sun tabbatar da kone tarin gidaje baya ga farwa juna tsakanin kabilun biyu masu rikici da juna.

Rahotanni sun ce yanzu haka rikicin ya haddasa gagarumar asara a kauyukan kabilun biyu ciki har da Wukari Kwatan Sule da Chonku da kuma iyakokin garuruwan Jootar da Vaase.

Shugaban kabilar Jukun Bako Benjamin ya shaidawa manema labarai cewa duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma da kabilar ta Tibi a makon jiya, har yanzu suna ci gaba da kawo musu farmaki.

A cewarsa da sanyin safiyar yau Asabar ne, ‘yan kabilar ta Tibi suka sake farmakar, kauyukan na su tare da kone gidaje baya ga kisan wasu mutane 15 matakin da ya sanya matasan kabilar ta Jukun mayar da martini.

Rahotanni sun ce ko a alhamis din da ta gabata makamancin rikicin ya hallaka mutane 12.

Tuni dai Rundunar 'yan sanda jihar ta Taraba ta tabbatar da afkuwar rikicin inda ta ce jami'an na kokarin kwantar da hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.