Isa ga babban shafi
Tunisia

Shugaba Beji na Tunisia ya nemi bai wa matasa damar mulkar kasar

Shugaban Kasar Tunisia mai shekaru 92 a duniya, Beji Caid Essebsi, ya ce ko da sunan wasa baya tunannin sa ke tsayawa takarar zabe idan wa’adin sa na yanzu ya kare a watan Nuwamba mai zuwa, inda ya ke cewa lokaci ya yi da za a bai wa matasa damar shiga a dama da su.

Shugaba Beji Caid Essebsi na Tunusia
Shugaba Beji Caid Essebsi na Tunusia REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Yayin jawabi ga jam’iyyar sa ta Nidaa Tounes da ya kafa a shekarar 2012, shugaban yace baya tunanin sake yin takara, domin lokaci yayi da za’a budewa matasa kofa.

Essebsi wanda shi ne zababben shugaban kasar Tunisia na farko, ya bukaci 'ya'yan jam’iyyar su da su kauda banbance banbancen da ke tsakanin su wajen goyawa Firaministan sa Youssef Chahed baya don zama sabon shugaban kasa.

A ranar 17 ga watan Nuwamba ake shirin gudanar da zaben kasar, amma yanzu haka an samu rarrabuwar kawuna wajen tsayar da Yan takarar zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.