Isa ga babban shafi
Algeria

Yan Sandan Algeria sun watsa gungun masu zanga-zanga

Yan sanda a Algeria sun yi amfani da feshin ruwa, wajen watsa dubban ‘yan kasar da ke ci gaba da zanga-zangar neman tilastawa shugaba AbdelAzizi Bouteflika yin murabus.

Yan Sandan Algeria yayin arrangama da masu zanga-zanga.
Yan Sandan Algeria yayin arrangama da masu zanga-zanga. Reuters
Talla

A karshen makon nan dai ‘yan kasar ta Algeria da ke zanga-zangar sun fadadata zuwa neman sauya tsarin siyasa da shugabancin kasar, tare da bukatar ganin cewa ilahirin mukarraban shugaba Bouteflika suma sun yi murabus.

Zanga-zangar ta soma ne daga 22 ga watan Fabarairu domin nuna rashin amincewa da aniyar shugaba Bouteflika mai shekaru 82, ta neman zarcewa bisa wa’adai na biyar, duk da cewa yana fama da rashin lafiya.

A ranar Talata da ta gabata babban hafsan sojin Algeria Janar Ahmed Gaed Salah ya bukaci Majalisar zartaswa ta kundin tsarin mulkin kasar ta bayyana shugaba Abdelazizi Bouteflika a matsayin wanda ya gaza tafiyar da mulkin kasar, sai dai har yanzu, majalisar ba ta zauna kan bukatar ba.

Tuni dai jagororin masu zanga-zangar suka yi watsi da shirin sojojin kasar, tare da bukatar ganin duk wani na hannun daman Bouteflika yayi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.