Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaban Algeria ya yiwa gwamnatin kasar garambawul

Tsawon wata daya da soma zanga-zangar nuna adawa da wani sabon wa’adi na biyar da Shugaban kasar Algeria Abdel Aziz Bouteflika ya bukacin yan kasar sun sake zabar sa ,a yau lahadi nan aka sanar da yiwa gwamnatin kasar garambawul.

Shugaban kasar Algeria da babban hafsan sojan kasar
Shugaban kasar Algeria da babban hafsan sojan kasar Eric FEFERBERG, Farouk Batiche / AFP
Talla

Fadar Shugaban kasar ta nada wasu mutane 27 da aka dorawa nauyi tafiyar da gwamnatin kasar ,matakin da ake ganin an samar da shi don kwantar da hankulan masu zanga-zanga.

Sai dai duk da wadanan sauye-sauye masu zanga-zanga na kan bakar su don gani Shugaban kasar Abdel Aziz Bouteflika dake fama da rashin lafiya ya fice daga wanan kujera cikin gaggawa.

A Faransa haka zalika tsawon wata daya kenan da ake ci gaba da zanga –zanga adawa da Shugaba Abdel Aziz Bouteflika na Algeriya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.