Adadin Fulanin da mahara suka hallaka a Mali ya karu
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da wasu mafarauta suka kaiwa Fulani a Mali ya karu daga 134 zuwa 157, abinda ke nuna cewa harin, shi ne irinsa mafi muni a tarihin kasar.
Wallafawa ranar:
Kakakin gwamnatin kasar ta Mali Amadou Kotia ne ya bayyana karuwar adadin, tare da bayyana fargabar cewa akwai yiwuwar sake samun Karuwar yawan wadanda suka hallaka.
Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan wasu Yan bindiga sun kai hari kan barikin sojin Mali inda suka kashe 23 daga cikin su.
A ranar Lahadi da ta gabata, Gwamnatin Mali ta kori wasu manyan jami’an sojinta, sakamakon farmakin da aka kai kan kauyen Ogassogou da ke yankin tsakiyar kasar inda aka yiwa Fulanin kisan kiyashi
Zalika a farkon makon Gwamnatin ta Mali ta kuma rushe kungiyar Ambassagou ta mafarautan kabilar Dogon, wadanda ake zargi da kai kazamin harin.
Wadanda suka tsira sun zargi mafarautan kabilar Dogon da kai mumunan harin, kabilar da aka zarga da hallaka Fulani 37 a kauyen Koulogon da ke yankin tsakiyar kasar ta Mali cikin watan Janairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu