Isa ga babban shafi
Mozambique-Zimbabwe

An gano mutane fiye da 300 da guguwar Idai ta hallaka a Mozambique

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa na ci gaba da aikin ceto a yankunan da guguwar Idai ta shafa da ke kasashen Mozambique, Zimbabwe da kuma Malawi dai dai lokacin da adadin mutanen da suka mutu a Ibtila’in ya haura 300.

Wani yanki da guguwar Idai ta lalata a Mozambique
Wani yanki da guguwar Idai ta lalata a Mozambique REUTERS
Talla

Bayan samun tsagaitawar guguwar tsakanin jiya da yau, yanzu haka jami’an agajin na ci gaba da bin lungu da sako don ceto wadanda ke da sauran lumfashi tare da kuma da tattara gawarwakin wadanda suka rasa ransu a guguwar wadda ta haifar da ambaliyar ruwa.

Rahotanni sun ce jami’an agajin sun rabu da wadanda ke kai dauki ta jiragen Shalkwafta da kuma wadanda ke bin cikin ruwa ta hanyar amfani da kwale-kwale.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana guguwar ta Idai da mafi muni da ta afkawa kasashen na kudancin Afrika cikin fiye da shekaru 10, wadda kawo yanzu ta shafi fiye da mutane miliyan guda tare da raba wasu dubu 80 da gidajensu.

Kasar Afrika ta kudu da ta kai dauki da jiragen shalkwafta ta ce ta yi nasarar ceto mutane 34, yayinda shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ke cewa adadin ‘yan kasarsa da suka mutu a Ibtila’in sun kai 350 baya ga wadanda suka jikkata.

Jami’an agajin da ke aikin ceto a kasashen 3 na kudancin Afrika, sun ce akwai tarin rayuka da ke cikin hadari, wadanda ake fatan kai wa garesu.

A bangare guda shugaban Darikar Katlika na duniya Fafaroma Francis, ya mika sakon jaje ga daukacin wadanda ibtila’in ya shafa, inda ya bukaci taimaka musu da dukkan abin bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.