Bakonmu a Yau
Farfesa Aisha Abdul Ismaila ta Jami’ar Bayero kan matakin gwamnati na fara hukunta iyayen da basu sanya yara a Makaranta ba
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:12
Gwamnatin Najeriya ta ce nan bada dadewa ba za ta aiwatar da shirin gurfanar da iyayen da basa sanya ‘yayan su a makarantu, a yunkurin da ta ke yi na rage yawan yaran da basa zuwa makaranta a fadin kasar.Ministan ilimi Adamu Adamu, ya ce muddin ba su fara gurfanar da irin wadannan iyaye a kotu ana daure su ba, ba za’a iya magance matsalar da ake samu na yaran da basa zuwa makaranta ba, wadanda alkaluma suka nuna cewa sun zarce miliyan 10 a Najeriya. Domin sanin tasirin matakin, Ahmad Abba ya tattauna da Farfesa Aisha Abdul Ismaila na Jami’ar Bayero, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.