Isa ga babban shafi
Mozambique

Ambaliya ta mamaye birni da kauyukansa a Mozambique

Shugaban Mozambique Filipe Nyusi, ya ce adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon mahaukaciyar guguwa mai dauke da ruwan sama da ta afka wa kasar zai iya haura mutane dubu daya, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu daruruwan mutanen da ruwa ya yi awon gaba da su.

Wani sashi na birnin Beira da ek kasar Mozambique da ambaliyar ruwa ta mamaye, sakamakon guguwar Idai.
Wani sashi na birnin Beira da ek kasar Mozambique da ambaliyar ruwa ta mamaye, sakamakon guguwar Idai. AFP PHOTO/MISSION AVIATION FELLOWSHIP
Talla

A birnin Beira da ke tsakiyar kasar ta Mozombique guguwar ta fi yin ta’adi kafin ta wuce zuwa makociyar kasar wato Zimbabwe, inda a can ma alkalumma ke nuni da cewa adadin wadanda ta hallaka ya kusa 98, yayin da wasu sama da 200 suka jikkata.

Shugaban kasar ta Mozambique Filipe Nyusi, ya ce zuwa marecen jiya litinin an tsamo gawarwakin mutane 84 ne, amma lura da yadda illahirin birnin na Beira da kuma kauyukan da ke zagayensa ke tsundum a cikin ruwa, adadin mamatan zai iya haura dubu daya.

Har zuwa safiyar yau talata ana ci gaba da aikin ceto mutanen da wannan iftila’i ya shafa, inda wasu ke cigaba da rayuwa a kan bishiyoyi wasu kuwa akan rufin gidajen da ba su ida ruftawa ba.

Har zuwa yanzu dai birnin Beira mai yawan mutane sama da dubu 500 na a cikin ruwa ne makil, yayin da ma’aikata agaji ke kokarin isa ga jama’a domin ceto su

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.