Isa ga babban shafi
Kudancin Afrika

Guguwa ta tafka barna a Zimbabwe, Mozambique da Malawi

Kakkarfar guguwar da masana suka yiwa lakabi da Idai da ta tafka barna, bayan ratsa kasashen Mozambique da Malawi, ta isa wasu yankunan gabashin kasar Zimbabwe, inda ta hallaka mutane 31, ta kuma jikkata 40, zalika wasu sama da 100 suka bace.

Wani yankin tsakiyar kasar Mozambique, bayan isar kakkarfar guguwar Idai mai dauke da ruwan sama.
Wani yankin tsakiyar kasar Mozambique, bayan isar kakkarfar guguwar Idai mai dauke da ruwan sama. AFP
Talla

Majalisar dinkin duniya, ta ce guguwar ta shafi sama da mutane miliyan 1 da rabi, a dukkanin kasashen guda ukun da ta ratsa, inda ta lalata dubban gidaje, makarantu da asibitoci, tare da zaftare hanyoyi masu yawan gaske musamman a yankin Chimani-mani na Zimbabwe.

A Mozambique, guguwar ta hallaka akalla mutane 19 tare da jikkata wasu 70, bayan da ta ratsa kasar a ranar Alhamis cikin gudun kilomita 160 a sa’a guda, lamarin da ya haddasa murdawar igiyar teku zuwa mitoci tara a tsaye. Jami’ai a kasar ta Mozambique sun kara da cewa kafin saukar mahaukaciyar guguwar, ruwan sama mai karfin gaske a makon da ya kare, yayi sanadin hallakar mutane 66 tare da raba wasu dubu 17 da muhallansu.

A kasar Malawi kuwa, guguwar da ruwan sama mai karfi, sun yi sanadin mutuwar mutane 56, tare da lalata muhallan akalla mutane miliyan daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.