Isa ga babban shafi
Najeriya-AIDS

Adadin masu dauke da cutar HIV AIDS ya ragu a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an samu raguwar wadanda ke dauke da cutar HIV AIDs a kasar daga adadin kashi 2 da digo 8 zuwa kashi 1 da digo 4 a karshen shekarar 2018 dai dai da mutane miliyan 1 da dubu dari 9.

Yanzu haka dai adadin masu dauke da cutar a Najeriya ya ragu zuwa mutane miliyan da dubu dari tara a cewar rahoton
Yanzu haka dai adadin masu dauke da cutar a Najeriya ya ragu zuwa mutane miliyan da dubu dari tara a cewar rahoton Solacebase
Talla

Cikin jawaban da Muhammadu Buhari ke gabatarwa yayin bikin bayyana sakamakon bincike kan illa da kuma yaduwar cutar a Najeriya wadda aka kafa kwamitin gudanarwa a shekarar 2018, shugaban ya ce rahoton babban ci gaba ne ga bangaren lafiya.

A cewar shugaban, a shekarar 2014 Najeriya na da yawan masu dauke da cutar ta HIV AIDs da suka kai kashi 3 da digo daya, wanda kuma samun raguwarsa zuwa kashi 1 da digo 4 na nuni da cewa kasar na kan turbar yakar cutar nan da shekarar 2030 kamar yadda ta tsara.

Sai dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya ce har ayznu lokaci bai yi da za a fara murnar yakar cutar ba, sai dai rahoton na bana zai karawa bangaren lafiya gamsuwar cewar ana samun gagarumin ci gaba a yaki da cutar.

A watan Yunin bara ne gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da wani shirin yaki da cutukan HIV da AIDS da ciwon hanta rukunin B da C, wanda aka baza jami’ai fiye da dubu dari biyu da hamsin ga kananan hukumomin Najeriyar dari 774.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.