Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 21/05 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 21/05 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 21/05 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 21/05 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/05 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/05 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/05 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/05 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/05 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Adadin mamata ya kai 18 a ruftawar ginin Lagos

media Ayyukan agaji sakamakon ruftawar wani gini a birnin Lagos, 2019-03-13 RFI / Ahmed Abba

Alkaluma na baya-bayan nan na nuni da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya 18 sakamakon ruftawar wani gini mai hawa 4 a birnin Legas da ke kudun maso yammacin Najeriya, yayin da wasu akalla 41 suka samu raunuka.

Kwamishinan lafiya na jihar Legas Jide Idris shi ne ya sanar da wadannan alkalumma, inda ya tabbatar da cewa an ci gaba da aikin ceto har zuwa cikin daren larabar da ta gabata.

Wakilin sashen hausa na RFI da ya ziyarci inda lamarin ya faru, ya tarar da jami’an hukumar agajin gaggauwa da kuma na kwana-kwana na gudanar da aikin ceto, yayin da ake ya tabbatar da cewa ana jin karar mutane a karkashin tarkacen ginin amma ba tare da an samu damar gare su ba.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa asalin ginin hawa uku ne, kafin daga bisani mamallakinsa ya yanke shawarar dora wani gini a kansa, yayin da mahukunta a Legas ke cewa tuni aka bayar da umurnin rusa ginin amma ba tare da an aiwatar da umarnin ba.

Faduwar gidaje a Legas ya zama ruwan dare a Najeriya, inda a watan satumbar 2014, ginin coci mallakin TB Joshua ya rufta tare da hallaka mutane 116 cikin har da ‘yan asalin kasar Afirka ta Kudu 84.

A watan disambar 2016 kuwa, akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon ruftawar wani coci a Uyo da ke jihar Akwa Ibom.

Hawa na uku na wannan gini da ya rufta na kunshe ne da wata makarantar firamire da kuma sashen renon yara,  yayin da aka samu faruwar ruftawar gidaje a sassa da dama na kasar ciki har da birnin Abuja.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure