Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo-Ebola

'Yan Tawayen Mai Mai sun kai hari cibiyar kula da masu Ebola a Congo

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce, wasu 'Yan Tawayen kabilar Mai Mai dauke da makamai sun kai hari Cibiyar kula da masu fama da cutar Ebola da ke gabashin kasar a yau asabar, inda suka kashe dan Sanda guda lokacin da suka yi artabu da jami’an tsaro.

Harin na zuwa dai dai lokacin da Darakta Janar na hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirin kai ziyara cibiyar
Harin na zuwa dai dai lokacin da Darakta Janar na hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirin kai ziyara cibiyar JOHN WESSELS / AFP
Talla

Magajin Garin Butembo, Sylvian Kanyamanda Mbusa ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar tarwatsa maharan, sakamakon kara yawan su da aka yi bayan cinnawa ginin wuta a makon jiya..

Yau aka shirya cewar Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Tedros Adhanom Gebreyesus zai kai ziyara Cibiyar, sai dai kakakin hukumar ya ce harin ya jefa shakku kan ziyarar.

Kawo yanzu dai cutar Ebola ta hallaka akalla mutane 600 tun bayan barkewar ta a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.