Mutane 183 sun jikkata a zanga-zangar Algeria
Ma’aikatar lafiya ta Algeria, ta ce mutane 183 sun jikkata a zanga-zangar da dubban ‘yan kasar ke ci gaba da yi, ta adawa da tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika da ke neman wa’adi na 5.
Wallafawa ranar:
Tun a makon da ya gabata aka soma zanga-zangar a sassan kasar musamman a birnin Algiers, amma a ranar Juma’a ta yi karfi, lamarin da ya haifar da arrangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar da ke kokarin kutsawa harabar fadar gwamnatin kasar.
Zanga-zangar dai ita ce mafi girma da aka taba yi a Algeria cikin shekaru 8, bayan kadawar guguwar sauyi a kasashen Larabawa.
Bouteflika ya dare mulkin Algeria a shekarar 1999 zuwa yanzu, sai dai tun a 2013, ya daina fita bainar jama’a, bayan kamuwa da ciwon mutuwar barin jiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu