Isa ga babban shafi
Sahel-Ta'addanci

Shugabannin yankin Sahel na taro kan sauyin yanayi

Shugabannin Kasashen Yankin Sahel 17 sun fara wani taro kan yadda za’a samar da Dala biliyan 400 ga yankin domin rage radadin da ya ke fuskanta sakamakon sauyin yanayi.

Shugabannin yankin Sahel
Shugabannin yankin Sahel OLYMPIA DE MAISMONT / AFP
Talla

Shugaban taron kuma shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issofou ya bayyana cewar yankin na cigaba da fuskantar matsalar da bashi ya ke haifarwa ba.

Shugaba Issofou ya danganta matsalar tsaro da sauyin yanayi, abinda ya ce masana kimiya ke tabbatar da cewar sun shafi yadda rayuwar jama’a ta ke ayau.

Shugaban ya yi misali da rikicin boko haram wanda ya ce ya kai kusan shekaru 10 yanzu haka, kuma ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 27,000 a tafkin Chadi da kuma raba mutane kusan miliyan biyu da muhallin su.

Shi dai wannan taro wani cigaba ne daga taron da aka yi a Paris cikin shekarar 2015 wanda ya duba halin da mutanen Yankin Sahel ke ciki wanda ke da mutane kusan rabin biliyan.

Kasashen da ke halartar taron sun hada da Benin da Burkina Faso da Chadi da Kamaru da Cape Verde da Djibouti da Gambia da kuma Guinea.

Sauran sun hada da Habasha da Eritrea da Cote d’Ivoire da Mali da Mauritania da Nijar da Najeriya da Senegal da Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.